An kashe mutane 2 an raunata 8 a rikicin Manoma Makiyaya a Kebbi


Mutane 2 ne suka mutu yayinda wasu 8 suka jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Suru ta jihar Kebbi. Daily trust ta wallafa.

 Shugaban karamar hukumar Suru, Mohammed Lawal, wanda ya bayyana hakan a jiya a lokacin da yake zantawa da gwamna Nasiru Idris, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne da safiyar ranar Asabar, inda wasu manoma suka je gonakinsu suka hadu da makiyaya da shanunsu a gonakin.

 Ya ce, “Manoman sun tambayi makiyayan ko su ne suke lalata amfanin gonakinsu wanda hakan ya haifar da rikici a tsakaninsu.  An kashe mutane, an lalata dukiyoyi da gidaje.”

 Ya ce kauyukan da abin ya shafa sun hada da Kankure, Tunga Rimi, Tunga Mai Rakumi, Runhewan Dulmeru, Sabuwan Kendawa da Limarein.

 Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Bello Rilisco, da ya zakulo wadanda abin ya shafa tare da tallafa musu da kayayyakin abinci da sauran kayayyakin agaji.

 Ya ce, “Gwamna Nasiru ya kutsa kai cikin rikicin manoma da makiyaya a yankin Suru da Koko Besse na jihar domin dawo da zaman lafiya mai dorewa a cikin al’ummomin da rikicin ya shafa.

 "Ya kuma bayar da gudummawar N13m ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka samu raunuka a rikicin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN