An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba


Wata kungiyar goyon bayan APC karkashin inuwar ‘Progressive League of Youth Voters (PLYV)’, ta nuna damuwa cewa gwamnatin jihar Kano na shirya zanga-zanga don tayar da tarzoma a babban birnin jihar a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, rahoton Blueprint.

Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara na baya-bayan nan da ta tsige Gwamna Abba Yusuf daga kujerarsa. Legit Hausa ya wallafa.

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, a Abuja, Audu Usman Shuaibu, shugaban kungiyar na kasa ya bukaci hukumomin tsaro da su shiga lamarin sannan su kare mazauna Kano daga tashin hankali.

Shuaibu ya yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne don tsoratar da kwamitin Kotun Koli da ke jagorantar karar zaben gwamnan Kano da aka daukaka, ta yadda za a juya hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke nasara ya koma wajensu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN