Yadda wani Sanata ya yi wa shugaban Majalisar dattawa kaca-kaca a zauren majalisar


An samu hayaniya a zauren majalisar dokokin tarayya a ranar Talata bayan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da sabbin nade-nade na shugabannin marasa rinjaye. Legit Hausa ya wallafa.

Akpabio ya nada Abba Moro sanata mai wakiltar Benue ta Kudu a matsayin shugaban marasa rinjaye; da kuma Osita Ngwu, sanata mai wakiltar Enugu ta Yamma a matsayin bulalar marasa rinjaye.

Yan jam'iyyar PDP sun maye gurbin Simon Mwadkwon, sanata mai wakiltar Filato ta Arewa; da Darlington Nwokocha, sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya, The Cable ta ruwaito.

Jim kadan bayan da Akpabio ya kammala yin sanarwar da aka ce ta fito ne daga kusoshin ‘yan majalisar na bangaren marasa rinjaye, sai hatsaniya ta kaure a zauren majalisar, Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Tony Nwoye na LP, sanata mai wakiltar Anambra ta Arewa, ya ce rashin adalci ne shugaban majalisar dattawa ya zabi shugabanni ga bangaren ‘yan majalisar marasa rinjaye.

“Mu bayinka ne? Me yasa shugaban majalisar dattawa zai zabo mana shugabanni?”

Nwoye ya yiwa shugaban tsawa.

“Ka yi mafi munin hakan, yanzu ka kai mu makura, me hakan ke nufi ne? Wannan ba adalci ba ne, ba wai ina magana a kaina ba ne, batu ne akan shugabancin majalisar dattawa."

“Kowane lokaci, kune ke ci gaba da zabar mana jagorori. Mu bayinka ne? Yadda aka zabe ka haka muma zabar mu aka ayi, babban abin da za ka iya yi shi ne dakatar da ni."

- cewar Nwoye

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, tsohon ministan harkokin cikin gida kuma Sanata a karo na huÉ—u a inuwar PDP, Sanata Abba Moro, ya zama sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da naÉ—in a zauren majalisar dattawa da ke Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN