Abin tausayi bayan tsoho mai shekara 70 ya yi wa yarinya kurma yar shekara 15 fyade har ta mutu


Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Jihar Enugu ta tasa keyar wani tsoho mai shekaru 70, Anthony Mgbe zuwa gidan yari bisa zargin laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara 15.


 Wanda aka kashen mai suna Uchechukwu Onwuzuru, wanda aka ce kurma ce kuma bebiya, ta zubar da jini har ta mutu bayan da wanda ake zargin ya yi mata fyade.


 Tsohon ya fito daga Umuagu, karamar hukumar Inyi Oji-River a jihar, an kama shi ne a kan tuhume-tuhume biyu da ’yan sanda suka yi masa.


Bisa la’akari da girman laifin, kotun majistare ta ki amincewa da bukatar neman belin tsohon ta kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, 2023.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN