Yadda biri ya fasa cikin yaro dan shekara 10 da kumbar yatsarsa ya ciro hanjinsa ya mutu

  

Wani biri ya kashe wani yaro dan shekara 10 a kasar Indiya bayan ya yaga hanjinsa.

 ‘Yan sanda sun ce yaron mai suna Dipak Thakor, wasu gungun birai ne suka kashe shi a lokacin da shi da abokansa ke wasa a kusa da wani gidan ibada a Salki, wani karamin kauye da ke yammacin jihar Gujarat, a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

 A cewar Mail Online, wasu gungun birai sun kai masa hari tare da abokansa, kafin daya daga cikin dabbobin ya caka masa kumbar yatsarsa a cikinsa sakamakon haka hanjin yaron suka fito.

 An garzaya da yaron asibiti amma abin takaici ya rasu kafin likitoci su yi masa magani.

 'Hanjin sa ya fito a harin.  An garzaya da shi zuwa gidansu, daga bisani aka kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu a lokacin da aka isa da shi asibiti,' kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kafar yada labaran kasar.

 Jami’in ya kara da cewa wannan shi ne hari na uku da gungun birai suka kai a cikin wannan mako kadai.

 Jami'in gandun daji Vishal Chaudhary ya ce shi da tawagarsa sun jima suna kokarin kama dabbobin masu hadari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN