Yadda Yaro ɗan shekara 9 ya yi garkuwa da ƴar shekara 5 a jihar Bauchi


Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban ƙananan yara, Hajara Gidado, ta bayyana yadda wani yaro Almajiri ɗan shekara tara, wanda aka ɓoye sunansa, ya sace wata yarinya ƴar shekara biyar a gidan mahaifinta. Legit Hausa ya wallafa.


Ta bayyana hakan ne a wajen bude taron horar da malaman Tsangaya da na Islamiyya na kwanaki biyu a ɗakin taro na Sa’ad Abubakar da ke Hajj Camp a Bauchi, cewar rahoton The Nation.


Yaron, a cewarta tun asali an kawo shi ne domin neman ilimin addinin Islama daga jihar Kano zuwa Magama Gumau da ke ƙaramar hukumar Toro.


Ta ce daga baya ya samu tsohuwar wayar Android ta hanyar barace-barace sannan ya fara koyon yadda a ke aikata miyagun laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, rahoton Tribune ya tabbatar.


A kalamanta:

"Wata rana yana cikin bara, ya isa wani gida, sai ya haɗu da wata yarinya ƴar shekara biyar, ya ɗauke ta ya kai ta wata makaranta a garin. Bayan wasu sa'o'i sai yarinyar ta ji yunwa, shi ma ya ji yunwa. Don haka sai ya zagaya domin neman abin da su biyun za su ci."


"Ya yi ƙoƙarin samun lambar wayar mahaifin yarinyar, wanda ya daɗe yana neman yarinyar. Almajirin ya kira mahaifinta ya ce ya kawo Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa. Mahaifin yarinyar yayi biris dashi."


"Da yamma ya yanke shawarar mayar da yarinyar gidan da ya ɗauke ta. A hanya sai ya gamu da mahaifinta, ya tambaye shi inda ya samo yarinyar, sai ya shaida wa mahaifin cewa ya yi garkuwa da ita, kuma tun da mahaifin bai kawo kudin da ya nema ba, sai ya yanke shawarar mayar da ita."


Ta ce mahaifansa da malamin da aka kawo shi domin yin karatun addini a wajensa, sun bar shi a gidan gyara hali na ƙananan yara na Bauchi, inda yake zaman gyaran hali bayan kotu ta yanke masa hukunci kan laifin da ya aikata shekara uku da suka gabata.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN