'Za ta sauya taswirar Isra'ila'- Iran ta yi gargadin kai hari ta riga-kafi kan Isra'ila a cikin sa'o'i masu zuwa idan har ta ci gaba da kai hare-hare kan Gaza


Iran ta gargadi Isra'ila da cewa za ta iya kai harin riga-kafi cikin 'yan sa'o'i masu zuwa'  idan har Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hamas a Gaza.


 Tun bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da harin ba-zata kan Isra'ila a ranar 8 ga watan Oktoba, inda ta kashe fararen hula fiye da dubu daya tare da yin garkuwa da daruruwan yan Isra'ila, Isra'ila ta mayar da martani, inda ta kai hare-hare kan maboyar Hamas da ke Gaza tare da dakile mai, abinci da ruwa, a daidai lokacin da Isra'ila ke shirin mamaye Gaza.


 Iran a ranar Talata, 17 ga Oktoba ta yi gargadin cewa wakilan kasar da ke yammacin Asiya za su iya kai hare-hare kan Isra'ila "a cikin sa'o'i masu zuwa".

 Haka nan kuma yayin da yake ishara da ganawar da ya yi da babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a baya-bayan nan, ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa: A cikin sa'o'i masu zuwa, duk wani mataki na turjiya kan gwamnatin sahyoniyawa abu ne mai yiwuwa.

Shugabannin gwagwarmaya ba za su kyale gwamnatin sahyoniyawan ta yi duk abin da ta ga dama a Gaza ba, sannan ta koma wasu fagagen gwagwarmayar,” in ji Amirabdollahian.


 Ministan na Iran ya kara da cewa kasarsa ba ta ba da umarni ba ga kungiyoyin da Iran ke marawa baya a duk fadin yankin amma tana goyon bayansu.


 Amirabdollahian ya kuma yi barazanar idan yakin ya fadada zuwa wasu fagagen, “zai canza taswirar Isra’ila.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN