Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga sun kai kazamin hari gidan Ɗan Majalisar Arewa, sun tafi da Matarsa da 'Ya'yansaYan bindiga sun yi garkuwa da mata da ‘ya’ya biyu na dan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓar Ipaiye/Malete/Olooru a karamar hukumar Moro. Legit Hausa ya wallafa.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa maharan sun kutsa cikin gidan ɗan majalisar da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar daren jiya wayewar garin ranar Talata, 17 ga watan Oktoba.

Wani shugaban al'umma a Shao ya ce:

"Masu garkuwan sun zo ne da yawa, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka tasa ƙeywar wadanda abin ya shafa zuwa cikin dajin da ke kusa."

Har yanzu ba a san inda suke ba duk da cewa daya daga cikin 'yan bindigan ya tuntubi ‘yan uwa amma har yanzu bai nemi kudin fansa ba. Ya ce ba ya tare da sauran a dajin shiyasa ba su faɗi kuɗin da za a basu ba."

"Amma a halin da ake ciki ganzu an shawarci ɗan majalisar ya tashi daga garin ya koma wani wuri daban."

Yayin da aka tuntuɓi ɗan majalisar da wayar salula don jin ta bakinsa bai ɗaga kiran ba.


Amma shugaban ‘yan banga na jihar, Alhaji Ibrahim Saka, ya ce, “Eh gaskiya ne kuma mun tura da wasu daga cikin mutanen mu domin su tsefe dajin su ceto su."

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Vanguard ta rahoto kakakin 'yan sandan na cewa:

"Har yanzun ba bu cikakkun bayanai a ƙasa amma da zaran mun samu bayani zamu dawo gare ku," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN