Yara biyu sun mutu yayin da kwale-kwale ya kama wuta a cikin rafi dauke da jama'a a jihar Neja


An tabbatar da mutuwar wasu yara biyu sakamakon gobarar kwale-kwale a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja
.

 Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Salihu Garba, ya ce kwale-kwalen ya kama wuta ne biyo bayan wata matsala da injin ya samu, wanda ya sa wata jarkan manfetur ya kama wuta.

 Garba ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba, kuma jirgin na dauke da fasinjoji 145.

 Yace;

 “NSEMA ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar yara biyu tare da raunata mutane biyu a karamar hukumar Katcha.  Lamarin dai ya faru ne ranar 20/10/2023 da misalin karfe 6 na yamma inda injin kwale-kwalen ya kama wuta kuma ya sa man fetur da aka ajiye a cikin wata jarka a jirgin da ke dauke da mutane 145 ya kama wuta.

 “Mutanen ’yan kabilar Danbo ne a Jihar Kogi, suna kan hanyarsu ta dawowa daga Kasuwar Katcha.  Ya zuwa yanzu dai an gano gawar daya yayin da ake ci gaba da neman na biyun.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN