Ta tabbata DPO, Yan sanda 3 sun rasa ransu lokacin artabu domin dakile harin Yan fashi da makami kan Bankuna a Binuwai


Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ta tabbatar da cewa jami’in ‘yan sanda DPO mai kula da Otukpo CSP John Adikwu da wasu jami’an ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani mummunan fashin da aka yi a ranar Juma’a da rana a wani banki a karamar hukumar Otukpo.

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Asabar. PM News ya rahoto.

 Wasu gungun ‘yan fashi da makami a wani samame na hadin gwiwa a ranar Juma’a sun kai hari a rassan bankuna daban-daban guda biyar a garin Otukpo.

 Bankunan da abin ya shafa sun hada da: Access Bank, First Bank, Zenith Bank, United Bank for Africa (UBA) da Stanbic IBTC Bank.

 Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai sun yi artabu da ‘yan bindigar a kan hanyar Otukpo zuwa Taraku inda suka kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan.

 Da yake bayar da bayanai kan harin, Anene ya tabbatar da cewa sauran ‘yan fashin sun bar motocinsu suka gudu suka shiga daji.

 PPRO ya ce: “Jami’in ‘yan sanda na Otukpo, CSP John Adikwu da tawagarsa da ke yankin sun yi artabu da ‘yan fashi da makami amma suka kasa hana su kai farmaki a bankunan kafin ajali ya riskesu lokacin artabun.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN