Yanzu yanzu: Yaki ya barke, Hamas ta kai harin bazata, ta kashe mutum 40, wasu 779 sun sami rauni, ta harba rokoki 5000 zuwa kasar Isra'ila


Kungiyar Islama ta Falasdinawa, Hamas ta kaddamar da hari mafi girma a kan Isra'ila a safiyar ranar Asabar 7 ga watan Oktoba a wani harin ba-zata yayin da wasu mayakan Hamas suka tsallaka zuwa garuruwa daban-daban na Isra'ila yayin da ake ci gaba da harba manyan rokoki daga zirin Gaza zuwa cikin Isra'ila.

 A daidai lokacin rubuta wannan rahotu, an yi ta jin kararrakin gargadi (siren) a duk fadin kudanci da tsakiyar Isra'ila, ciki har da birnin Kudus.

 Akalla mutane 40 ne suka mutu tun bayan da kungiyar Hamas ta kai harin ba-zata kan Isra'ila, in ji hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar.

 An kuma jikkata wasu mutane 779 a cewar ma'aikatar lafiya ta Isra'ila.


 Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana kan wani mataki na yaki kuma ministan tsaron kasar ya ce kungiyar Hamas da ke samun goyon bayan Iran ta yi babban kuskure ta hanyar ayyana yaki a kan Isra'ila, a matsayin ramuwar gayya, sojojin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare ta sama a Gaza.


 Ministan tsaron Isra'ila Gallant ya ce Hamas ta kaddamar da yaki da kasar Isra'ila.  "Sojojin Isra'ila suna yakar abokan gaba a kowane wuri", in ji shi.


Harin dai ya yi nuni da kutsawa da wasu ‘yan bindigar Hamas da ba a san adadinsu ba zuwa cikin Isra’ila daga yankin Gaza, kuma daya daga cikin mafi muni a rikicin Isra’ila da Falasdinu a cikin shekaru da dama da suka gabata.

 Kafofin yada labaran Isra'ila sun rawaito an gwabza fada tsakanin mayakan Falasdinawa da jami'an tsaro a garuruwan kudancin Isra'ila.  

 A Gaza, jama'a sun yi tururuwa don siyan kayayyaki tsammanin cewa za a iya daukar kwanaki ana yaki a gaba.  Wasu sun fice daga gidajensu sun nufi matsuguni don samun kariya daga hare-hare.


 Kwamandan sojin Hamas, Mohammad Deif ne ya sanar da fara yakin a wani shiri da aka watsa a kafar yada labaran Hamas, inda ya yi kira ga Falasdinawa a ko'ina su yi shiga yakin.


"Wannan ita ce yaki mafi girma don kawo karshen mamayar da aka yi a duniya," in ji shi, ya kara da cewa an harba rokoki 5,000 zuwa cikin Isra'ila.


Kafofin yada labaran Falasdinu sun rawaito cewa mayakan sun yi awon gaba da wasu Isra'ilawa da dama sannan kuma kafar yada labaran Hamas ta yada faifan bidiyo da ke nuna tankar Isra'ila da mayakan Hamas suka lalata.


 Firayim Isra'ila Minista Benjamin Netanyahu a jawabin da ya yi a safiyar yau ya ce kasar na cikin yaki.  Ofishinsa ya ce zai gana da manyan jami’an tsaro nan da sa’o’i masu zuwa.


 Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta ce mayakanta na tare da Hamas a harin.


 "Muna cikin wannan yakin, mayakanmu suna kafada da kafada da 'yan uwansu dake cikin dakarun Qassam Briged har sai an samu nasara," in ji kakakin kungiyar Islamic Jihad Abu Hamza a wani sako da ya wallafa a kafar sadarwar zamani ta Telegram.


 Harin dai ya zo ne kwana guda bayan da Isra'ila ta yi bikin cika shekaru 50 na yakin 1973 da ya kai kasar ga mummunan fatara a wani harin ba-zata da Siriya da Masar suka kai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN