Kotu ta yankewa wani dan Sokoto, Ahmad Abubakar Ahmad hukuncin daurin shekaru 87 a gidan yari, bisa samunsa da laifin damfarar mutane 12 kudade daban-daban da sunan sa hannun jari a ofishinsa na canji.
A cewar EFCC Ahmad ya kuma yi wa wadanda abin ya shafa alkawarin basu jari daga kashi 50% zuwa 100% na jarin su duk wata, amma ya kasa, bai basu jarin da suka zuba ba bai kuma mayar musu da kudadensu ba.
EFCC ta yi zargin cewa Ahmad ya damfari wadanda abin ya shafa kan kudi Naira miliyan 325 ta hanyar damfara.
EFCC ta gano wasu daga cikin manyan mutanen da zamban Ahmad ya rutsa da su da suka hada da Usama Abdullahi wanda ya ba shi kudi har Naira miliyan 80 don saka hannun jari da Najib Hamza, wanda kuma ya ba shi Naira miliyan 50 don wannan manufa.
Da aka gurfanar da shi a gaban kotu, Ahmad ya amsa laifuka 12 da ake zarginsa da aikatawa wanda ya sa jami’in EFCC, Kufre Ekpeyoung ya roki kotu ta yanke masa hukunci.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Hamza Liman ya roki Kotu ta yi masa sassauci saboda cewa wannan shi ne laifin farko.
Daga nan sai mai shari’a Dogondaji ya yanke wa Abubakar hukuncin daurin shekaru 87 a gidan yari tare da zabin tarar N200,000.00 (Naira Dubu Dari Biyu) akan kowanne caji da aka yi masa da ya bayar da jimillar kudi N2,400.000.00 (Naira miliyan biyu da dari hudu).
Ya kuma ba da umarnin a mayar da Naira 225,661,000 (Miliyan Dari biyu da Ashirin da Biyar Naira Dubu Dari Shida da Sittin da Daya) ga duk wadanda suka shigar da kara, ta hannun EFCC.
DAGA ISYAKU.COM