Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta musanta janye karar da ta shigar a kan karar zaben gwamnan Kano da ake yi.
Jaridar Vanguard to rahoto Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitinta kan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Ya ce jami’in shari’a na hukumar, wanda ake zargin ya janye daga shari’ar, an dau matakin ladabtarwa a kansa.
Ya ce: “An jawo hankalin Hukumar kan rahotannin kafafen yada labarai bisa wata wasika da jami’in shari’a na ofishinmu na Jihar Kano ya rubuta cewa hukumar ta janye daga karar da ta shigar a kan karar da ake yi na zaben Gwamnan Kano.
“Muna so mu bayyana sarai cewa wasiÆ™ar ba ta da izini. Tuni dai aka janye shi kuma jami’in yana fuskantar matakin ladabtarwa.
“Don haka ana shawartar jama’a da su yi watsi da zancen janyewar hukumar daga shari'ar".
“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa inda masu shigar da kara suka sa INEC a cikin wani lamarin shari'ar, hukumar tana da hakkin ta mayar da martani.
“Saboda haka, mun umurci lauyoyinmu da su ci gaba da bin ka’idojin Hukumar. Manufar ba ta canza ba."
DAGA ISYAKU.COM