Idan ba a manta ba a ranar Talata 24 ga watan Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari fadar Sarkin Maru, Abubakar Maigari da ke karamar hukumar Maru a jihar, inda ‘yan sanda suka dakile harin.
Abin baƙin ciki, an kashe mutum ɗaya. Marigayin dai an bayyana sunan sa da Malam Ukashatu, wani mutum ne da ke zaune a gefen fadar.
‘Yan fashin sun kuma yi awon gaba da wani jami’in IT.
Sannan kuma a daren Alhamis, 26 ga watan Oktoba, an ce ‘yan ta’addan sun koma fadar domin neman sarkin.
Ba su same shi ba sai suka afkawa gidaje a unguwar suna nemansa inda suka kashe mutum hudu a cikin lamarin.
A yau 27 ga watan Oktoba ne aka gudanar da sallar jana'izar wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.