Jerin Laifuffukan da Hukumar EFCC ke bincikar Godwin Emefiele a kansu


Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a ranar Juma'a, 27 ta fara gudanar da cikakken bincike kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
. Legit Hausa ya wallafa

Babban abin da hukumar ke bincikar Emefiele a kansa shi ne bashin dala biliyan 15 da aka ciyo daga ƙasashen ƙetare, rahoton TheNation ya tabbatar.

Emefiele zai kuma yi bayanin yadda babban bankin ya kashe Naira biliyan 74.84 wajen samarwa da fitar da kuɗaɗe ciki har da sabbin takardun kuɗi na Naira.

Zarge-zargen dai ƙari ne kan zargin zamba wanda jami’in bincike na musamman, Jim Obazee, wanda ke duba ayyukan CBN ya bankaɗo.

Obazee, wanda kwamitinsa ke haɗa kai da hukumar binciken ƴan sandan Najeriya, ya kuma miƙa rahoton wucin gadi kan CBN ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

An tabbatar da cewa, kwamitin jami'an EFCC ya fara bincikar Emefiele kan zarge-zargen da ake masa, waɗanda suka haɗa da:

Wani majiya daga EFCC ta ƙara da cewa:

“Emefiele yana hannunmu kuma tuni ya ke amsa tambayoyi kan wasu batutuwa ko zarge-zargen da ake yi masa daga wata tawagar da ke ƙarƙashin kulawar daraktan ayyuka, Abdulkarim Chukkol."

"A matsayinmu na hukuma, ba za mu yi magana a kan lamarinsa ba domin kada mu kawo cikas ga binciken da ake yi."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN