Wani dan daba mai suna “Abba Burakita” da aka bayyana ana nema ruwa a jallo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da mabiyansa guda 40.
Idan ba a manta ba a baya kwamishinan ‘yan sandan jihar CP ya bayyana cewa ana neman Abba da wasu manyan ‘yan daba guda biyu tare da yin alkawarin bayar da tukuicin Naira 100,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023, ya ce Abba Barakita da son ransa ya mika kansa ga ‘yan sanda tare da sanar da tuba daga ayyukan ‘yan daba.