Yan bindiga sun yi wa wani Hakimi mugun aiki da zai baka tausayi a jihar Neja


Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe Malam Usman Sarki, hakimin garin Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.


 Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne a Zazzaga da kauyukan da ke makwabtaka da su a daren Talata, 10 ga Oktoba, 2023.


 Majiyar ta ce an kuma yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba da suka hada da mata.


 “An kai harin ne cikin dare ranar Talata.  Sun harbe Hakimin kauyen na Zazzaga, Malam Usman Sarki har lahira tare da yin garkuwa da wasu da dama,” inji majiyar.


 “A yanzu, ba za mu iya bayar da ainihin adadin mutanen da suka tafi da su ba.  Sun kuma yi awon gaba da shanu da awaki da tumaki da yawa namu.”


 Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan harin da ake zargin an kai ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN