Dakarun Sojoji Sun Tono Bama-Bamai a Wurin da Bam Ya Halaka Rayuka Sama da 1,000 a Najeriya


Hukumar sojin Najeriya ta ƙara tono ababen fashewa a wurin da Bam ya tashi shekaru 21 da watanni tara da suka gabata a Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Hukumar sojin ƙasa ta Najerriya ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta naanhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya. Legit Hausa ya wallafa.

Tashin bama-baman wanda ya auku ranar 27 ga watan Janairu, 2002 a sansanin sojoji da ke Ikeja, ana kyautata zaton ya halaka mutane aƙalla 1,100 yayin da wasu sama da 20,000 suka rasa mahallansu.

Bayan haka tashin Bama-baman ya jikkata dubbannin mutane tare da jefa wazu da dama cikin halin kaƙanikayi.

An ce Bama-bamai da wasu ababen fashewa sun tashi ne bisa kuskure a cikin sashin ajiye makamai na barikin sojoji sama da shekaru 21 da suka wuce.

Fashewar wadda ta yi kara kusan sau bakwai, cikin kwanaki biyu, ta yi sanadin lalata dukiyoyi a yankin da kewaye. Lamarin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Da yake jawabi a Legas ranar Talata yayin kaddamar da shirin tsaftace wurin, babban Hafsan Sojojin ƙasa (COAS), Laftanar-Janar Tajudeen Lagbaja, ya ce a karshe rundunar aikin kwashe abinda ya rage.

COAS ya bayyana cewa rundunar soji ta fara jigilar sauran bama-bamai da ababen fashewar da ba su fashe ba a wancan lokacin zuwa daya daga cikin sansanonin ta da ke Ajilete, jihar Ogun.

Ya ce aikin share da tsaftace wurin na farko da aka yi a shekarar 2002 ya ƙara tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Ikeja da kewaye.

Lagbaja ya ƙara da cewa sun gano wasu bama-bamai da ba su fashe ba a wurin da ibtila'in ya faru kuma hakan ne ya nuna akwai buƙatar sake tsaftace wurin a yanzu.

"Ina ƙara tabbatar wa yan Najeriya musamman mazauna Legas da Ogun cewa za a gudanar da wannan aiki cikin ƙwarewa da kuma taka tsantsan da bin matakan da ya dace."

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN