Daga karshe, an daure Janar na soji shekara 7 a Kurkuku bayan kotun soji ta same shi da laifin sata


Wata kotun sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, ta yanke wa wani tsohon Manajan Darakta na Nigerian Army Properties Limited, Maj.-Gen.  Umar Mohammed, daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kudi dala miliyan 2,178,900 da kuma naira biliyan 1.65 mallakin hukumar sojin Najeriya (NAPL).

 Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an yankewa Mohammed hukuncin ne bayan kotu ta same shi da laifuka 14 daga cikin tuhume-tuhume 18 da aka gabatar a gaban kotun, kan, almubazzaranci da kudade, da kuma hada baki da dai sauransu.  Sai dai wanda ake zargin a baya ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

 A zaman da aka ci gaba a yau inda aka yanke hukunci, kwamitin mutum takwas karkashin jagorancin Maj.-Gen.  James Myam ya bayyana cewa an samu babban hafsan sojan da laifi aka yanke masa hukuncin a cikin tuhume-tuhume 14 cikin 18.

 Myam ya ce an gabatar da kara na daya a karkashin sashe na 383(1) na dokar laifuka ta Cap c38 ta tarayyar Najeriya, kuma hukuncin da ya dace a sashi na 390 (7), ya kara da cewa an gabatar da tuhumar ne bisa sashe na 114 na dokokin jami'an tsaro.  Cap A20 2004.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN