Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 50 da suka hada da wani hakimi da mata da kananan yara a kauyen Bagega da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.
An bayar da rahoton cewa an kashe mutanen kauyen uku a harin da aka kai da safiyar Talata, 17 ga Oktoba, 2023.
Wasu daga cikin mazauna kauyen da suka tabbatar wa jaridar Punch faruwar lamarin, sun ce ‘yan bindigar da suka hau babura sun far wa kauyen, inda suka yi harbe-harbe tare da kona gidaje da dama.
Da yake tabbatar da harin, hakimin kauyen,Abubakar Uba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da hakimin gundumar kafin su ci gaba da yin garkuwa da mutane da dama a kauyen.
“Sun afkawa kauyen ne a kan babura da dama, kuma zangon farko da suka yi shi ne gidan hakimin, wasu kadan daga cikinsu sun tafi da shi tare da wasu mutanen gidansa guda uku kafin su shiga cikin garin kuma suka kara yin barna.” Inji Uba.
From ISYAKU.COM