Kasurgumin dan ta'adda da ya addabi mutane a Arewa ya mika wuya ga sojojin NajeriyaRundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa wani kasurgumin kwamandan kungiyar ta'addanci na Boko Haram, mai suna Bulama Bukar, ya mika wuya ga dakarunta a yankin Gubio, jihar Borno. Legit ya wallafa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta labarai na rundunar soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya saki a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a Abuja.

Jaridar Daily Nigerian a rahoto cewa dan ta'addan da ya mika wuya ya kasance kwamandan sansanin Boko Haram a Tapkin Chad da ke kauyen Gilima a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Ya kara da cewar:

Kayayyakin da aka samo daga dan ta'addan da ya mika wuya sun hada da bindigar AK 47 guda daya, makamai 5, harsasai 7.62mm guda 44, wuka daya, babur daya da kudi N23,500.

"A yanzu haka, ana daukar bayanan dan ta'addan."

A halin da ake ciki, kakakin rundunar sojin ya ce dakarun soji na nan suna aikin bude wuta domin raba kasar da tsagerun yan ta'adda, masu tayar da kayar baya da sauran miyagu a fadin kasar.

Mista Nwachukwu ya ce a kan haka ne dakarun bataliya ta 2 suka kai kautan bauna kan wasu yan ta'adda a yankin Udawa dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar 17 ga watan Oktoba sannan suka sheke yan ta'adda uku.

Ya ce wutan da aka bude masu ya sa sauran sun tsere, yayin da sojojin suka kwato wata bindiga dauke da harsashi 111 , babura biyu, babban rediyon sadarwa mai karfin gaske da kuma wayoyi guda biyu.

A cewarsa, wani soja ya rasa ransa a yayin arangamar, rahoton Leadership.

Ya kara da cewar a wannan ranar, dakarun Birgediya ta 1 sun kama wani da ake zargin yana kai alburusai a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana hanyar kai wa wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Gishiri harsashi ne.

A cewarsa, dakarun yan banga sun kwato wata jaka dauke da harsashin 7.62mm guda 224, wayar hannu daya da kuma kudi naira 4,000 daga hannunsa.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN