An kashe wani Malamin addinin Islama da wasu mutane biyu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani Masallaci a kauyen Ga Allah Babba, kusa da Sabon Layi a cikin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna a safiyar ranar Talata, 24 ga watan Oktoba.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari a Masallatan ne a lokacin da suke gudanar da sallar asuba.
An ce ‘yan bindigar suna dawowa ne daga jihar Zamfara ta dajin Kamuku da ke kusa da kauyen Kuriga, sai suka ga Musulmin da suke sallar asuba. Nan take ‘yan bindigar suka rufe Masallacin tare da bude wuta kan masu ibada, inda suka kashe babban limamin da wasu mutane biyu.
“An kai harin ne a Ga Allah Babba da ke Sabon Layi, wata al’ummar manoma a yammacin Birnin-Gwari. Wadannan yankuna ne da ke makwabtaka da dajin Kamuku da dajin Kuyebana a jihohin Zamfara da Neja. An kashe limamin wani Masallaci da wasu masallata biyu. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Talata. Wasu Masallata biyu da suka samu munanan raunuka an kaisu babban asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari. Kusan kullum ‘yan bindiga sukan kai hari a yankin Birnin-Gwari, suna kashewa tare da yin garkuwa da mazauna yankin, musamman manoma. Lamarin ya fi kamari kan babbar hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna kuma ya zama ruwan dare ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar,” wani shugaban al’umma, Zubair Abdurrauf, ya ce.
From ISYAKU.COM