A wani samame na sahihanci da suka kai kan 'yan ta'addan da ke jihar Sakkwato, sojojin runduna ta 8 ta Garrison sun tarwatsa Yan bindigan a kauyen Tukandu, inda suka watse gungun 'yan ta'adda da suka yi kaurin suna wajen aikata munanan ayyuka a yankin baki daya.
Jami'in hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun yi aikin ne a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, 2023.
“Mummunan harin da sojojin suka kai ya kawo karshen ‘yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga. A wani samame da sojojin suka kai sun kwato bindigu kirar AK-47 guda uku, Bindigar PKT daya, harsashi na musamman 125 mm 7.62, roka 2 da bama-bamai da kuma babura guda 9.” Inji shi.
“Shugaban hafsan soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojojin, inda ya bukace su da su jajirce tare da ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addan domin murkushe su tare da hana su ‘yancin daukar mataki.”
From ISYAKU.COM