Yakin Isra'ila da Hamas: Saudiyya ta gayyaci Najeriya da sauran kasashen OIC zuwa taron gaggawa


Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya kira taron gaggawa na kasashe mambobin kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC. Daily trust ta wallafa.

 OIC ita ce kungiya ta biyu mafi girma bayan Majalisar Dinkin Duniya da ke da kasashe 57 ciki har da Najeriya, ta bazu a nahiyoyi hudu.  Kungiyar ita ce muryar gamayya ta al'ummar musulmi.

 A cewar wata sanarwa da aka buga a shafin intanet na OIC a ranar Lahadi, an shirya taron ne a ranakun 18 da 19 ga Oktoba a Jeddah, Saudi Arabia.

 An kira taron gaggawar ne domin tattauna rikicin da ke faruwa a zirin Gaza tsakanin Hamas da Isra'ila.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN