Sanata Elisha Abbo ya yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shirya makarkashiyar tsige shi da kotun daukaka kara ta yi.
Abbo ya yi wannan zargin ne a gidansa da ke Abuja, a jiya, sa’o’i bayan kotun daukaka kara ta soke zaben sa na Sanata. Vanguard ya wallafa.
Sanatan na Adamawa ya yi ikirarin cewa, Akpabio kuma yana da shirin tsige dan Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu da wasu Sanatoci hudu saboda rashin goyon bayan takararsa na Shugabancin Majalisar.
Abbo ya bayyana hukuncin da aka yanke masa a matsayin juyin mulki ga dimokradiyya amma ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu.
Sanatan ya dage cewa duk da kotu ta ayyana Amos Yohanna na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu.
A cewarsa, ya doke dan takarar PDP da tazarar kuri’u 11,000.
Kotun daukaka kara, a wani mataki na bai daya da wasu alkalai uku suka yanke, ta yi watsi da hukuncin kotun da tun farko ta tabbatar da Abbo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe kujerar Sanata.
Ta bayyana cewa akwai cancanta a cikin karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Amos Yohanna, ya shigar a zaben.
From ISYAKU.COM