Yadda wata bazawara ke tura ruwa a baro tana sayarwa domin ta ciyar da yayanta marayu 6 a jihar Kano


Wata mata ‘yar Najeriya mai matsakaicin shekaru, Gambo Haruna, wacce mijinta ya rasu shekaru shida da suka gabata bayan ya sha fama da jinya, ta kwashe shekaru biyu tana tura baro, tana sayar da ruwan da za ta kula da ‘ya’yanta shida, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

 Tana zaune a gidan haya a wani tsohon gidan laka, tana zaune a daki daya, wanda take biyan Naira 12,000 duk shekara a Gadar Katako, yankin Rimin Kebe a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.

 Rayuwa ta yi matuƙar wahala ga wannan mata yar fiye da shekaru 30.  Kuma ta rungumi duk wani ƙalubalen da ta fuskanta a rayuwa.

 Gambo ta ce ta yi aiki dare da rana domin ta kula da ‘ya’yanta saboda ba za ta so yin bara ko yin wani abu da ya sabawa doka ba.

 Sai dai ta ce halin da take ciki ikon Allah ne, kuma ta yi addu’a don ganin Allah ya kawo mata dauki cikin wannan yanayi.

Dangane da harkar sayar da ruwa da kuma kalubalen da take fuskanta, Gambo ta ce tana bukatar karin kuzari, inda ta ce a kullum tana samun kudi tsakanin Naira 750 zuwa 1,000, inda daga nan ta rika biyan N150 ga mai baro da ta karbi haya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN