Babbar Kotun Tarayya da ke Sakkwato, karkashin Mai Shari’a Ahmad Mahmud, ta yanke wa wani hakimi, Alhaji Umar Mohammed (aka Dan Bala) hukuncin daurin shekara biyar da rabi a gidan yari bisa zarge-zarge hudu da suka hada da mallaka da kuma sayar da tabar wiwi kilo 436.38 da kuma 7kgs magungunan sa maye da hukumar NDLEA ta gurfanar da shi a Oktoban 2022.
An yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu akan kowane tuhume-tuhume na 1 da 2 tare da zabin tarar Naira miliyan 1, da kuma wata takwas akan kowanne, yahin da na 3 da 4 ba tare da zabin tara ba. PM News ta rahoto.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
DAGA ISYAKU.COM