Yadda Isra'ila ta jefa dubban al'ummar Gaza cikin matsanancin matsalar rashin ruwa


Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu ta ce a yanzu ruwa ya zama “la’amari na rayuwa da mutuwa” ga mutanen yankin Zirin Gaza bayan da Isra’ila ta katse ruwan da suke samarwa.


 Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a yankin Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta fada a ranar Asabar cewa sama da mutane miliyan biyu ne ke cikin hadari sakamakon karewar ruwa. Aljazeera ta rahoto.


 “Ya zama batun rayuwa da mutuwa.  Ya zama dole: ana bukatar isar da man fetur a Gaza a yanzu domin samar da ruwa ga mutane miliyan biyu,” in ji Kwamishinan UNRWA Janar Philippe Lazzarini.


 Ba a ba da izinin shigar da kayan agaji zuwa Gaza tsawon mako guda ba, a cewar hukumar.


 Ruwa mai tsafta ya kare a Zirin Gaza yayin da tashar ruw cibiyoyin ruwan jama'a suka daina aiki.  A yanzu dai an tilastawa Falasdinawa amfani da gurbataccen ruwa daga rijiyoyi, lamarin da ke kara barazanar kamuwa da cututtuka.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN