Yadda wasu mutane biyu suka makale suka mutu a cikin tankin diesel a Kano


Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyu bayan da suka makale kuma suka shake har lahira a lokacin da suke aikin share tankar dizal a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba.


 Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne kan hanyar Katsina kusa da Shataletalen Baban Gwari a karamar hukumar Fagge da ke jijar Kano.


 Ya bayyana sunayen wadanda suka mutu a matsayin Philip Osando mai shekaru 40 da kuma Philip Emmanuel mai shekaru 35. Ya ce sun shiga tankin ne don sharewa amma suka kasa fitowa.


 Ya ce jami’an kashe gobara ne suka dauko wadanda abin ya shafa suka mika su ga ‘yan sanda aka kai su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN