An yi wa Malamar jami'ar FUTMinna yankan rago a gidanta a birnin Minna jihar Neja


An tsinci gawar wata malamar Sashen Biochemistry na Makarantar Kimiyyar Rayuwa ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) Minna a Jihar Neja, Dokta (Mrs) Adefolalu Funmilola Sherifat da aka yanka a gidanta da ke Unguwar Gbaiko a garin. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.


 Channels TV ta ruwaito cewa shugaban kungiyar malaman jami’a (ASUU) a makarantar Farfesa Gbolahan Bolarin ya ce ,an gano gawar marigayiyar ne a safiyar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, lokacin da mabiya cocin ta suka bi ta gidanta bayan ba a gan ta a lokacin hidimar ibada ba.


 Wasu mazauna garin sun ce bayan da aka bude kofar gidanta, an same ta a cikin jininta kuma an yi mata yankan rago a makogwaronta da wukake a gefenta.  Daga baya hukumomin ‘yan sanda sun dauke gawar zuwa dakin ajiyar gawa.


 Kafin rasuwarta, tana zaune tare da wata mai yi mata hidima, amma ta sallami yarinyar a ranar Juma’a, 27 ga Oktoba.


 Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba kafin lokacin rubuta wannan rahotu.


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN