Yadda wasu hatsabiban matasa 3 suka sace Kambu, hula, sandan sarautar Sarki cikin dare


Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar din da ta gabata ta ce jami’anta sun kama Amusa Kazeem, Oke Oladipupo da kuma Johnson Oluwole bisa laifin satar Hular rawanin da sandan sarautan ofishin marigayi Olu na Ogunmakin, Oba Olugbenga Shodiya, wanda ya rasu kimanin watanni biyu da suka gabata.

 Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola ya fitar ya ce Kazeem, Oladipupo da Oluwole a ranar 12 ga watan Oktoba da misalin karfe 2 na safe, sun shiga gidan marigayin suka sace Hular rawanin da sandar sarauta. Vanguard ta rahoto.

 Sanarwar ta ce "A ranar 12 ga Oktoba, 2023, an samu bayanan sirri daga fadar Mai Martaba Sarkin Ogunmakin cewa wani mai suna Amusa Kazeem "m" Oke Oladipupo da Johnson Oluwole 'm' sun hada baki tare da sace Hula, rawani da sandan Sarauta.  watanni bayan rasuwar Sarki Ogunmakin.

 “ Wadanda ake zargin sun shiga gidan ne da misalin karfe 2 na safe suka je inda aka ajiye kadarorin marigayi sarki.  Mutanen biyu sun dauki mabudin inda aka ajiye shi a hannun wanda aka ba shi domin ya ajiye kadarorin kuma suka cire Hula, rawani da sandan saurauta na marigayi Sarki wani aiki da aka bayyana a matsayin abin kyama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN