Dubun ta cika na Likitan bogi da ke ziyartar asibitin Zamfara yana duba matsalar al'aurar mata har da matan aure


Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta kama wani likitan bogi da ya bayyana kansa a matsayin likitan mata da ke aiki da asibitin kwararru na Yarima Bakura da ke Gusau.


 Jami’in hulda da jama’a na hukumar, SC Ikor Oche, a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023, ya gabatar da wanda ake zargin mai suna Muhammad Naziru Mode, bisa laifin aikata wani aiki da ya sabawa sashi na 484 na kundin laifuffukan jihar.


 Kakakin ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri.


 A cewar Oche, wanda ake zargin mai shekaru 26 wanda ya kira kansa “Dr.  IBB” ya ziyarci asibitin a kullum domin kula da marasa lafiya, musamman a wuraren kula da mata.

Ya ce wanda aka kama yana duba matsalolin al'aurar mata ne har da matan aure kafin dubunsa ta cika. Ya ce za a gurfanar da Likitan bogin a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN