Shugaba Bola Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar gudanarwa na hukumar kula da hanyoyin tarayya (FERMA) na tsawon shekaru hudu.
An yaba wa shugaba Tinubu saboda nada matasa da yawa cikin majalisarsa. A baya dai ya yi alkawarin cewa matasan za su taimaka wa gwamnatin sa.
Engr. Imam Ibrahim Kashim Imam matashi ne dan shekara 24 da haihuwa, an haife shi a watan Disambar 1998. Ya kammala karatunsa a jami'ar Brighton da ke kasar Burtaniya inda ya yi digiri na farko a fannin injiniya.
Matashin mai farin jini ya samu digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Brighton kuma ya kammala bautar kasa (NYSC) a watan Agustan 2022.
Kafin nadin nasa da shugaba Tinubu yayi, Imam Muhammed ya kasance mataimaki na musamman ga ministan ayyuka kuma tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi.
DAGA ISYAKU.COM