Yadda uwargida ta zuba wa maigida tafasashshen man gyada yana cikin barci kuma ta kwada masa guduma ta gudu


Wata mata mai suna Hope Nwala ta zubawa mijinta mai auna Ekelediri Nwankwo tafasashshen man gyada a yankin Okehi da ke karamar hukumar Etche a jihar Ribas
.


 An tattaro cewa ma’auratan sun samu matsala kan hali da yanayin sa suturar kanwar matar da ke zaune tare da su.


 Hope, wanda ta fito daga al’ummar Obite a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a jihar, ta gudu daga Okehi bayan da ta aikata wannan danyen aiki.


 Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, 2023, wanda abin ya shafa ya ce surukarsa ta yi masa rashin mutunci tare da sanya tufafin da bai dace ba don haka ya yanke shawarar tura ta gida.


 Nwankwo ya ce ya ba ta wasu kudi domin ta koma gida, sai dai matarsa ​​ta ki amincewa da matakin da ya dauka, lamarin da ya janyo cece-kuce mai zafi tsakanin ma’auratan.


 Ya bayyana cewa a zaman surukar sa a gidansu, matarsa ​​ta fara aikata munanan halaye.  Ya ce ya dade yana lura da wani bakon mutumin da ke lababe a kusa da matarsa ​​da sirikarsa.


 Nwankwo ya ce ya jajirce ya kuma fuskanci matarsa ​​game da abin da ya gani, inda ya bukaci ya san ko wane ne bakon mutumin, amma sai ta mayar da lamarin tashin hankali ta zuba masa tafasashshen mai a lokacin da yake barci bayan ta kwada masa guduma.

Kakakin hukumar yan sandan jihar SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce yan sanda sun fara bincike da kuma farautar matar da ta tsere bayan ta aikata laifin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN