Yan sanda sun kama matar da ta kwara wa mijinta tafasashshen man gyada ta kwada masa guduma ta guduRundunar 'yan sanda a jihar Ribas ta sanar da cafke matar da ta yi wa mijinta wanka da tafasasshen man gyada a jihar.

Matar mai suna Hope Nwala ana zargin ta da watsawa mijinta, Ekelediri Nwanko man gyada kan wata karamar jayayya, cewar Punch.

Nwala ta aikata laifin ne a kauyen Okehi da ke karamar hukumar Etche a jihar bayan mijin ya kwanta bacci. Legit Hausa ya wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce matar na hannun jami'ansu, Newstral ta tattaro.

Grace ta ce jami'ansu sun yi nasarar kama matar ce bayan ta tsere ganin girman laifin da ta aikata.

Ta ce:

"An kama matar kuma ta na hannun jami'anmu, an cafke ta ne a yau Alhamis 12 ga watan Oktoba.
"A yanzu haka ana kan bincike wanda da zarar an kammala za a dauki matakin da ya dace."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN