Bawa ya yi murabus, Tinubu ya nada sabon shugaban EFCC, bayanai sun fito


Shugaba Bola Tinubu ya nada wani lauya Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

 Nadin nasa na wa’adin shekaru hudu ne a matakin farko, har sai majalisar dattawa ta ta batar da shi, a cewar Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Tinubu. PM News ya rahoto.

 Nadin Olukoyede ya biyo bayan murabus din da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da aka dakatar, Mista Abdulrasheed Bawa ya yi.

 Olukoyede lauya ne wanda ke da shekaru sama da ashirin da biyu (22) na gogewa a matsayin mai ba da shawara kan bin ka'ida kuma kwararre kan binciken zamba da bayanan kamfanoni.

 Yana da gogewa a harkokin hukumar EFCC, inda ya taba rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban hukumar (2016-2018) da kuma sakataren hukumar (2018-2023).

 Don haka, ya cika sharuddan da doka ta gindaya na nada shi a matsayin Shugaban Hukumar EFCC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN