Kar ki rika duba wayoyin mijinki – Kwankwaso ya shawarci ma’aurata a wajen daurin auren gata a Kano


Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party a zaben 2023, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shawarci ma’aurata 1,800 da ke karkashin shirin auren gata a Kano da su guji duba wayar ma’aurata miji ko mata.

 Da yake jawabi a wajen liyafar da gwamnatin jihar ta shirya wa ma’auratan a dakin taro na Open Theater da ke gidan gwamnatin Kano a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, Kwankwaso ya bayyana cewa irin wadannan abubuwa na iya kawo karshen aure.

 Yace;

 “An yi muku nasiha da kowa da kowa.  Na yi imani an yi muku nasiha sau dubu.  Malamai da iyaye da ’yan uwa da ma ’yan kasuwa sun yi muku nasiha kan yadda za ku zauna lafiya da juna.

 “Amma ina da shawara guda ɗaya gare ku;  wato duba wayoyin juna.  Kada ku leka wayar juna domin wannan shi ne babban dalilin rabuwar aure a kwanakin nan.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN