Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani da ake zargi da kisan kai mai suna Usman Yahaya Muhammed, wanda ya kashe wani dan acaba tare da sace babur dinsa a karamar hukumar Mokwa da ke jihar.
Wanda ake zargin, wanda É—an banga ne na yankin, ya kaahe Dan acaban ne ranar Juma’a, 29 ga Satumba, 2023, ya saci babur É—in da nufin ya sayar da shi kuma ya tara kuÉ—i don bikin aurensa.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya gabatar da wanda ake zargin a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, tare da wasu da aka kama bisa laifuka daban-daban a jihar.
“A ranar 1/10/2023 da misalin karfe 0830, an samu labarin cewa an tsinci gawa wanda aka yankewa makogwaro jina-jina a unguwar Shabalile da ke Mokwa. Jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO reshen Mokwa sun ke wurin da lamarin ya faru inda suka dauki gawar zuwa dakin ajiye gawa na Asibiti,” in ji PPRO.
“A binciken da ake yi a ranar 2/10/2023 da misalin karfe 1130, an gano wani babur Bajaj da ake zargin an yi wa mamacin fashi ne a wani gini da ba a kammala ba a Mokwa, yayin da bincike ya kai ga kama wani Usman Yahaya Muhammed mai shekara 20 na kauyen Kinboku-Kudu a Mokwa
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya ce ya hau babur din zuwa kauyen Eppa, kuma a kan hanyar su ne ya tsayar da mahayin ya yi masa sare shi har lahira. Ya jefar da gawar ya tafi da babur. Ana binciken lamarin a SCID Minna.”
Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya ce an shirya daurin auren nasa ne ranar Juma’a sannan kuma ya amsa laifin aikata irin wadannan laifuka sau takwas a baya.
DAGA ISYAKU.COM