Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wata matar aure ‘yar shekara 18 mai suna Khadija Adamu da laifin lakada wa diyar kishiyarta ‘yar shekara 5 duka har lahira a yankin Kandahar da ke jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, 2023, yayin wata ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Bauchi.
CP Muhammed ya ce an kama Khadija ne bayan da wani Abdulaziz Adamu ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa wadda ake zargin ta lakada wa Hafsat Garba dukan tsiya, sakamakon haka ta samu munanan raunuka kuma likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) ya tabbatar da rasuwarta.
A cewar Kwamishinan, wanda ake zargin ta amsa laifinta ba tare da gardama ba.
Ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da ita a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.
DAGA ISYAKU.COM