Wata Mata ta cefanar da Jikanta dan wata 3 a kasuwa saboda tsabagen talauci


Wata mata ta siyar da jikanta mai watanni uku a duniya a kan kuɗi N50,000 a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya. Legit Hausa ya wallafa.

Wacce ake zargin Oluchukwu Nwosu ta siyar da jaririn ne ba tare da sanar da ɗiyarta Ijeoma ba, wacce ta haifi yaron ba tare da aure ba, cewar rahoton Premium Times.

Chidinma Ikeanyionwu, hadimar kwamishiniyar mata da walwalar jama'a a jihar, Ify Obinabo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.

Ikeanyionwu ta ce a yanzu kwamishinan ta ceto yaron, sannan ta kuma taimaka wajen sanya ƴan sanda cafke wacce ake zargin.

Wacce ake zargin, Mrs Nwosu, da take magana bayan ta shiga hannu, ta yi iƙirarin cewa halin talauci da kasa kula da jaririn ne ya tilasta mata siyar da shi.

Matar ta ce wannan shi ne karo na uku da diyarta ta haihu ba tare da aure ba, inda ta yi nuni da cewa akwai wasu yara biyu dukkaninsu maza, ana kula da su a wani gidan marayu da ke birnin Awka.

Ta ce tun daga lokacin da diyarta ta haifi yaron da ƙyar suke samun abin da za su ci, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ta yi iƙirarin cewa wani mutum mai suna Tochukwu Asiegbu ya tuntuɓe ta inda ya amince ya sayi yaron a kan farashin N50,000.

A nasa ɓangaren, Mista Asiegbu, wanda aka ruwaito ya sake sayar da yaron, ya ce ya samu ribar Naira 30,000 ne kawai daga siyan jaririn.

Sai dai Evelyn Egwuatu, wacce aka ɗauko jaririn daga hannunta, ta ce ta biya wata mata Ebelechukwu Uba kudi N200,000 domin ta siyo yaron.

An Tsinci Jariri Cikin Tsumma

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN