Shugaban Hukumar Tsaro Ya Ajiye Aiki Kan Zargin Alaka da ‘Yan Bindiga Daga Nada Shi


Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin da zai kafa jami’an tsaron sa kai, Garba Moyi Isa ya yi murabus. Legit Hausa ya wallafa.

Rahoto ya zo daga Leadership cewa Kanal Garba Moyi Isa mai ritaya ya sauka daga kujerar da gwamnatin jihar Sokoto ta nemi daura shi.

Garba Moyi Isa ya yi murabus ne bayan ‘yan awanni da rantsar da kwamitinsa mai mutum 25 a yunkurin an kawo zaman lafiya a Sokoto.

Ana tunani tsohon sojan ya dauki wannan mataki ne saboda wani bidiyo da aka fitar, ana zargin ya na da alaka da ‘yan ta’addan da ke Sokoto.

Garba Moyi wanda ya rike kujerar Kwamishina har sau uku a jihar Sokoto, ya tara manema labarai a karshen makon jiya, ya yi jawabi.

Tsohon jami’in tsaron ya yi bayanin yadda ya bautawa kasarsa na shekara da shekaru a gidan soja, daga baya kuma ya shigo siyasa.

Ko a rahoton da aka samu daga jaridar Punch, haka dai aka ji cewa Moyi bai bada asalin abin da ya jawo ya ajiye kujerar da aka ba shi ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN