Fitacciyar jarumar shirya fina-finai a masana'antar Nollywood da ke Najeriya, Tonto Dikeh, ta canza sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jam'iyyar APC ta kasa ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa tare da Hotuna shafinta na manhajar X wacce aka fi sani da Twitter a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, 2023. Legit ya wallafa.
A cewar sanarwan da jam'iyya mai mulki ta fitar, Jarumar ta tabbatar da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance ne ranar Litinin ɗin nan da muke ciki.
Shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Mary Alile tare da mataimakin sakataren watsa labaran jam'iyyar ta ƙasa, Duro Meseko, ne suka karɓi jarumar.
Jigan-jigan sun tarbi shahararriyar jarumar a hukumance a heskwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
From ISYAKU.COM