An kama mutane hudu da ake zargi da fashin banki a Benue da ya yi sanadin mutuwar DPO, yan sanda 3


A ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da jami’an ‘yan sandan Najeriya, da na sojojin Najeriya da dai sauransu, sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a fashin bankin Benue da ya yi sanadin mutuwar wasu jami’an ‘yan sanda a kan hanyar Otukpo-  Taraku a jihar Binuwai.


 Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa jaridar Punch cewa;


 “Jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kama wasu ‘yan fashi da makami hudu a kan hanyar Otukpo-Taraku, jihar Benue a ranar Asabar.  ‘Yan fashin na daga cikin ‘yan fashi da makami da suka kai hari a bankuna da ofishin ‘yan sanda a Otukpo a jihar Binuwai.”


 Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta bukaci manema labarai da su jira kammala binciken da rundunar ta ke gudanar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN