Wasu shugabannin matasa sun yi wa wata mata mai suna Obot Udo Ekpo bulala bisa zarginta da satar wasu hannun plantain guda uku a kauyen Okon Eket da ke jihar Akwa Ibom. Shafin isyaku.com ya samo.
An tattaro cewa an kama wanda ake zargin ne a safiyar Litinin, 16 ga Oktoba, 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa ta so ta sayar da plantain da ta sace a babbar kasuwar Urua Udo Inyang da ake ci a mako-mako, wanda a yau ne, amma sai aka kamata dumu-dumu.
Wanda ake zargin wanda ta fito daga Ikot Akpandem a Okon Eket, shugaban matasan kauyen, Akparawa Uyai Udo Jacob, ya mika ta ga ‘yan sanda da ke yankin Uqua domin bincike da gurfanar da ita gaban kuliya.
From ISYAKU.COM