Rikici tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Kwanga da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdullahi Buhari Warah ya bayyana cewa kisan da wasu mutane da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wani manomi a gonarsa, ya kai ga harin ramuwar gayya a wani kauyen Fulani inda wasu fusatattun mutane suka kashe wani karamin yaro. Daily Post ta rahoto.
A cewarsa, “Fadan ya samo asali ne sakamakon barnata amfanin gona da shanu suka yi, kuma ya yi sanadin arangama, inda mutane biyu suka mutu.”
Ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya a yankin.
A cewarsa, ba a kama kowa ba domin manoman da makiyayan sun bar yankin ne kafin isowar jami’an tsaro.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, da aka tuntube shi, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.
DAGA ISYAKU.COM