Gwamnatin Tarayya za ta sake fara shirin Tradermoni a watan Nuwamba inda kowane mai cin gajiyar shirin zai samu Naira 50,000 don tallafa wa kasuwancinsa.
Yayin da shirin rancen bai bashi da ruwa ga ‘yan kasuwa – wanda aka fara a shekarar 2018. Ministar harkokin jin kai da kawar da talauci Mrs Betta Edu ta ce gwamnati na shirin sake kaddamar da shi. Channels TV ta rahoto.
Da take tabbatar da cewa ba a soke tsarin ba, ta ce: “Yanzu, a karon farko, wanda za mu fara a watan Nuwamba, za mu zabi babbar kasuwa guda daya a kowane yanki na majalisar dattawa. Kasuwanni 109 kenan kuma za mu shiga kasuwanni, za mu samo ‘yan kasuwa a cikin shagunansu a cikin kasuwanni.
Ba kamar Naira 10,000 da ake baiwa ‘yan kasuwa a lokutan farko ba, akwai karin kudi ga masu cin gajiyar.
"N50,000 za mu tallafa wa kasuwancinsu," in ji ta a cikin wani shiri ranar Lahadi a Channels Television.
DAGA ISYAKU.COM