Yadda uwargida ta sha guba ta mutu saboda mijinta ya yi wa dadironsa cikin gaba da fatiha


Wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Misis Bose Odunayo, ta kashe kanta a jihar Ondo saboda budurwar mijinta.

 An tattaro cewa lamarin ya faru ne a unguwar Igoba dake Akure, babban birnin jihar Ondo.

 A cewar jaridar mallakin gwamnatin jihar, an ruwaito cewa mahaifiyar ‘ya’ya hudu ta sha maganin kwari ne bayan da ta samu kiran barazana daga daya daga cikin dadiron mijinta da ta yi ikirarin cewa ta dauke masa ciki.

 An samu labarin cewa an kwashi yan kallo lokacin da iyalan mamacin suka zo da gawarta kwatsam daga garin Akoko domin yi mata jana’iza a gidan mijinta da ke Akure, inda ake gudanar da addu'oi kafin a binne gawar.

 Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa marigayiyar wadda ta sha guba a gidanta da ke unguwar Igoba a Akure, nan take ta nufi garinsu da ke Ifira Akoko, domin sanar da iyayenta cewa mijin nata zai yi sanadin mutuwarta ba tare da wani bata lokaci ba sakamakon huldarsa da yar dadiro.

 A cewar wata majiya daga dangin, kafin marigayiyar ta mitu, ta ce dadiron mijinta ta zarge ta da laifin zubar da cikin da ta samu.


 Mijin wanda mamba ne na kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa, NURTW, a Akure, ya ce marigayiyar matarsa ​​ta dauki kayan ta tafi garin iyayenta da ke Akoko, sai kawai ya ji labarin rasuwar ta.

 "Matata ta yi ikirarin cewa ita ce ke kula da duk wasu kudade a gidan da suka hada da biyan kudin makarantar yara wanda a zahiri ba gaskiya ba ne," in ji shi.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN