Minista ya yanke jiki ya fadi a gaban Majalisar Dattawa suna tantance shi, bayanai sun bayyana bayan ya farfado


Balarabe Abbas Lawal ya fadi ana tsaka da tantance shi a yau Laraba 4 ga watan Oktoba a Abuja wanda shi ne ya maye gurbin Nasir El-Rufai.

Faduwarshi ke da wuya aka kawo masa dauki inda bayan farfadowa da ya yi, ya shaidawa shugaban majalisar, Godswill Akpabio dalilin faduwar tashi.

Balarabe ya ce tsantsar gajiya da ya yi ne ta jawo masa wannan suma inda ya ce ya shafe kwanaki uku ya na aiki ba hutawa, Aminiya ta tattaro.

Majalisar ta tantance ministoci uku da su ka hada da Balarabe Abbas daga jihar Kaduna da Dakta Jamila Ibrahim daga Kwara da kuma Ayodele Olawanda daga jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN