Abun kunya: Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar da Janar gaban Kotun soji kan zargin satar $1,476,200Wata kotun Soji ta musamman da rundunar sojin Najeriya ta kafa ta samu tsohon Manajan Darakta kuma Mataimakin Shugaban Kamfanin Sojojin Najeriya, Manjo Janar Umar Muazu Mohammed da laifuffuka 14 cikin 18 da ake zarginsu da aikatawa wadanda duk sun saba wa dokar aiki.

 Laifukan sun hada da sata, jabu, hada baki, da karkatar da kadarorin Sojoji ba tare da izini ba da dai sauransu kuma dukkansu suna karkashin horon aiki. Rahotun Jaridar Vanguard.

 Daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi masa har da karbar dala 1.045,400 da kamfanonin sufurin jiragen ruwa suka biya don amfani da Jetty na sojojin Najeriya da ke lamba 6 Marina, Victoria Island, Legas.

 An kuma samu Manjo Janar UM Mohammed da laifin satar dala $430.800 na wasu kudade da aka biya a asusun ajiyar Sojojin Najeriya da ke bankin Unity, Abuja domin amfani da Jetty na Sojojin Najeriya, Marina, VI, Legas.

 Bugu da kari kuma, an samu Manjo Janar Mohammed da laifin janyewa tare da kwace makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 74 daga cikin miliyan 75 da aka biya na wani kadarori na sojojin Najeriya a Ikoyi, Legas.

 Sai dai ba a samu Janar din ba da laifi kan zargin da ake masa na sayar da kadarorin Sojoji da ya kai Naira miliyan 200 a Legas tare da sace wasu Naira miliyan 750 daga cikin Naira Biliyan 2.5 da aka samu a bankuna da kuma gudummawar da aka samu daga masu biyan kudin gidaje na Sojoji.  Asokoro, Abuja

 Har ila yau, ba a same shi da laifin yin jabun takardar yarjejeniya ba bisa zargin kwace wani kadarorin Sojoji a Legas.

 Kotun Soji ta musamman na karkashin Manjo Janar Kames Myam a matsayin shugaba, tana da wasu Manjo Janar guda bakwai (7) a matsayin membobi da kuma Birgediya Janar a matsayin lauya kuma ana sa ran za ta karanta hukuncin da ta yanke wa wadanda ake tuhuma zuwa ranar Talatar mako mai zuwa.

 A lokacin da ake zaman kotun, an shigar da Manjo Janar UM Mohammed a gaban kotun a kan kujera, amma shugaban kotun, Manjo Janar Myan ya ce an gudanar da duk wani bincike na lafiyar wanda ake zargin kuma duk sun tabbatar da cewa ya cancanta a gurfanar da shi gaban kuliya.

 Babban Lauyan masu gabatar da kara shi ne Col BA Oguntayo (Rtd) yayin da Jagoran Lauyan Tsaro ya kasance Olalekan Ojo, SAN.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN