Da duminsa: An kori dan sanda daga aiki bayan ya yi wa yar shekara 16 fyade da dare a lokacin da take tsare a ofishin Yan sanda


Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta kori Dan sanda mai suna Belasa Iyangedue, bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 16 fyade, mai suna Nguemo Terkaa, yayin da take tsare.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bartholomew Onyeka ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba a Makurdi.

 CP Onyeka ya ce dan sandan da aka kora ya aikata laifin a ofishin ‘yan sanda na Tse Agbaragba, da ke karamar hukumar Konshisha.  Ya kara da cewa jami’in da aka kora tuni ya fuskanci tuhuma.

Tum farko a ranar 15 ga watan Agusta aka tsare yarinyar saboda laifin bata ma wani suna.

 A yayin da take tsare, an zargi dan sandan ya dauke ta daga dakin da take ciki da daddare, inda ya shigar da ita daya daga cikin ofis tare da yi mata fyade.

Washegari bayan an bayar da belin wadda aka yi wa fyaden, ta kai rahoto ga DPO, inda aka kama dan sandan kuma aka shigar da karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar a Makurdi.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Bartholomew Onyeka, ya ce, “Dan sandan da aka kora ya aikata laifin a ofishin ‘yan sanda na Tse Agbaragba, karamar hukumar Konshisha.

 “’Yan sanda hukuma ce mai da’a kuma kasancewarta hukuma ce da ke da alhakin dakile aikata laifuka da yaki da laifuka, ba a yarda irin wadannan mutane su zauna a cikin tsarin ba.

 "Ba kawai an kore shi ba, yana fuskantar tuhuma."

 Wannan zargin fyaden ya zo ne kasa da shekara guda bayan da abokansa suka yi bikin Belasa Iyangedue a dandalin sada zumunta na Facebook biyo bayan faretin kammala samun horon aikin dan sanda da ya yi bayan ya kwashe watanni yana samun horon aikin ‘yan sanda.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN